Dollar

38,1303

0.12 %

Euro

43,6723

1.37 %

Gram Gold

4.079,8900

3.15 %

Quarter Gold

6.731,9300

3.38 %

Silver

40,3700

1.95 %

Amnesty ta koka kan cewa da yawan waɗanda abin ya shafa sun kasa guduwa – ciki har da yara da tsofaffi – wanda sakamakon hakan ‘yan bindigar suka yi musu kisan gilla suka bar su cikin jini kace-kace.

Amnesty International ta yi Allah wadai da sake kashe mutum 51 da ‘yan bindiga suka yi a Filato

Ƙungiyar Kare Hakkin Ɗan’adam ta Amnesty International ta yi kakkausan Allah wadai da kisan aƙalla mutum 51 da aka sake yi a jihar Filaton Nijeriya sakamakon harin ‘yan bindiga suka kai ƙauyen Zikke.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun kai harin ƙauyen ne da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Bassa a cikin daren Litinin, sannan suka ƙona wasu ƙauyukan da dama tare da yin sace-sace da ma lalata duk wani abu da suka ci karo da shi.

Amnesty ta koka kan cewa da yawan waɗanda abin ya shafa sun kasa guduwa – ciki har da yara da tsofaffi – wanda sakamakon hakan ‘yan bindigar suka yi musu kisan gilla suka bar su cikin jini kace-kace.

“Dole ne a binciki gazawar hukumomi kuma a daina yi musu uzuri saboda yadda wasarere din da suke yi wa sha’anin tsaro ke haifar da waɗannan munanan hare-hare, makonni biyu bayan kashe mutum 52,” in ji Amnesty.

Ƙungiyar kare hakkin ɗan’adam ɗin ta ƙara da cewa “yin Allah kawai da wadannan munanan hare-haren bai wadatar ba kuma dole ne a nuna jajircewar kare al'umma ta hanyar tabbatar da adalci.

“A yayin da Shugaba Tinubu ke ikirarin cewa gwamnatinsa tana sanya sabbin matakan tsaro don magance ƙaruwar rashin tsaro a ƙasar, hare-hare na bayan nan a jihar Filato na nuna cewa dukkan matakan tsaron da ake ɗauka ba sa aiki,” ta ce.

Ƙungiyar ta ba da alkaluma na yawan mutanen da aka kashe a jihar Filato daga Disamban 2023 zuwa Fabrairun 2024, inda ta ce an kashe mutum 1,336.

Daga cikin wadanda aka kashe 533 mata ne sai yara 263, sannan maza manya 540.

Kazalika ta ce fiye da mutum 29,554 ne suka rasa matsugunansu, daga cikinsu 13,093 yara ne yayin da mata 16,461 suka rasa matsugunansu.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#