Sport
Dollar
38,1588
0.3 %Euro
43,6101
1.61 %Gram Gold
3.958,7400
2.25 %Quarter Gold
6.529,2600
2.67 %Silver
39,4700
3.6 %Ganau sun ce lamarin ya faru ne a Gidan Kaji da ke ƙaramar hukumar Konduga a yayin da motocin da sojoji suke yi wa rakiya suke kan hanyar komawa Maiduguri daga Damboa.
Wasu abubuwan fashewa da ake zargi mayaƙan Boko Haram sun binne sun fashe a kan hanyar Maiduguri-Damboa a Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Nijeriya, inda suka yi sanadin mutuwar aƙalla mutum takwas ranar Asabar.
Ganau sun ce lamarin ya faru ne a Gidan Kaji da ke ƙaramar hukumar Konduga a yayin da motocin da sojoji suke yi wa rakiya suka taka abubuwan fashewa kan hanyar komawa Maiduguri daga Damboa.
Mutum 14 sun jikkata sakamakon wannan lamari, a cewar gidan talbijin na Nijeriya, NTA.
Ya ƙara da cewa gwamnan jihar Borno Babagana Zulum ya ziyarci asibitin ƙwararru na Maiduguri inda ake kula da lafiyar mutanen da suka jikkata.
Gwamnan ya tabbatar musu cewa hukumomi za su biya kuɗaɗen magungunansu tare da bai wa kowane mutum da ke jinya naira dubu hamsin a matsayin tallafi.
Wannan hari na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan gwamnan ya bayyana cewar sabbin hare-haren Boko Haram da garkuwa da mutane a garuruwa a kusan a kowace rana ba tare da tunkarar ‘yan ta’addar ba na nuna cewa ana cin jihar tasa da yaƙi.
Gwamna Zulum yana nuna damuwa game da yadda hare-haren baya bayan nan ke fatattakar cibiyoyin jami’an tsaro a Wajirko, da Sabon Gari a karamar hukumar Damboa, da Wulgo a Gamboru Ngala, da Izge a ƙaramar hukumar Gwoza da ma wasu yankunan, inda aka samu asarar rayukan fararen-hula da ba su ji ba ba su gani ba da ma jami’an tsaro.
Zulum ya ƙara da cewa wannan hali da aka tsinci kai a ciki na sanya matukar damuwa da bayyana koma-baya a jihar Borno da ma yankin arewa maso gabashin Nijeriya.
Comments
No comments Yet
Comment