Sport
Dollar
38,0502
0.04 %Euro
43,2418
0.01 %Gram Gold
3.945,8500
0.49 %Quarter Gold
6.469,8500
0 %Silver
39,4900
-0.24 %Wannan sanarwa na zuwa ne bayan zargin da wasu manyan ’yan siyasar ƙasar suka yi wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu cewa yana nuna ɓangaranci a rabon muƙaman siyasa da yake yi.
Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta jaddada aniyarta ta haɗin-kan ƙasa da yin adalci wajen naɗa muƙamai a ƙasar, a cewar Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (OSGF) a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a
Wannan sanarwa na zuwa ne bayan zargin da wasu manyan ’yan siyasar ƙasar suka yi wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu cewa yana nuna ɓangaranci a rabon muƙaman siyasa da yake yi.
Cikin masu wannan zargi har da Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Atiku Abubakar da kuma Sanata Muhammad Ali Ndume wanda yake wakiltar shiyyar kudancin Jihar Borno a Majalisar Dattawan Nijeriya.
“Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (OSGF) na son yin magana game da maganganun da ake ta yaɗawa a baya bayan nan, musamman a shafukan sada zumunta, dangane da yadda ake naɗa muƙaman tarayya.
“Gwamnati na ƙaryata ikirarin na jahilci tare da jaddada sadaukarwarta ga ƙa'idojin adalci da daidaito da haɗin-kan ƙasa. Dukkan naɗe-naɗe ana yin su ne bisa tsarin rabon muƙamai na tarayya, kamar yadda ya zo a sashe na 14 na kundin tsarin mulkin tarayyar Nijeriya na 1999 (kamar yadda aka sauya),” in ji sanarwar.
Ofishin OSGF ya ce ya kamata a lura cewa Shugaba Tinubu ya yi amanna da haɗin-kan Nijeriya, kuma yana bin aƙidun adalci da tsarin adalci a dukkan naɗe-naɗen muƙamai.
“Wannan Gwamnati ta himmatu wajen tabbatar da cewa dukkan yankuna da na al’umma na ƙasar nan sun samu isassun wakilci a cibiyoyi da hukumominta,” a cewar OSGF.
Ya kuma ce duk wanda ke da ƙorafi a kan mas’alar to ya miƙa zuwa ga Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya wanda shi ke da ruwa da tsaki a kan irin waɗannan muƙamai.
Daga ƙarshe Ofishin na OSGGF ya yi kira ga al’umma da su yi watsi da duk wasu jita-jita su dogara da sanarwar hukuma don samun sahihan bayanai.
Sannan ta jaddada aniyarta ta tabbatar da samar da ci-gaba da haɗin-kai a Nijeriya.
Comments
No comments Yet
Comment