Dollar

38,0519

0.04 %

Euro

43,2362

0.03 %

Gram Gold

3.941,6100

0.38 %

Quarter Gold

6.469,8500

0 %

Silver

39,4100

-0.44 %

Gwaska ya kasance mataimakin wani jagoran ‘yan bindiga mai alaƙa da ISWAP.

Sojojin Nijeriya sun kashe ƙasurgumin ɗan bindiga Gwaska da 'yan bindiga 100 a Katsina

An kashe ƙasurgumin ɗan bingida mai suna Gwaska a jihar Katsina tare da wasu 100 a wani harin da sojoji suka ƙaddamar kan masu aikata miyagun laifuka a jihar da ke arewa masu yammacin Nijeriya.

Kwamishinan Tsaro da Lamuran Cikin Gida na Jihar, Dr. Nasir Mua’zu, ne ya bayyana wannan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a.

Ya ce aikin na soji wani muhimmin ɓangare ne na dabaru da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro ke bi wajen dawo da zaman lafiya a Jihar Katsina da Arewa Maso Yammacin ƙasar.

A lokacin harin, dakarun sun ƙwato tare da lalata bindigogi masu jigida biyu da bindigogi da aka ƙera a gida biyu da sauran makamai domin hana masu aikata miyagun laifuka sake amfani da su.

Ya bayyana cewa runduna ta 17 ta sojin Nijeriya tare da ɓangaren sojin saman ƙasar ne suka ƙaddamar da hare-haren ranar 10 ga watan Afrilun shekarar 2025 a dabar ɓarayin daji a Mununu Bakai da Zango da Jeka Arera da Malali, da kuma Ruwan Godiya duka a cikin ƙananan hukumomin Kankara da Faskari.

“Hare-haren da suka yi daidai kan ɓarayin, bisa bayanan sirrin da aka samu, sun yi silar kashe wani wanda ake nema ruwa-a-jallo da aka fi sani da Gwaska, wanda mataimaki ne ga wani shugaban ‘yan bindiga mai alaƙa da ISWAP,” in ji shi.

“Bayanan sirri sun tabbatar da cewa kwanan nan ne Gwaska ya ƙaura daga ƙaramar hukumar Danmusa zuwa dajin Munumu.

“A iya cewa wannan aikin ya yi nasarar katse ayyukan masu aikata miyagun laifukan da suka daɗe suna aikata ta’addanci a ƙauyuka da garuruwa da ke ƙananan hukumomin Faskari da Kankara da Bakori da Malumfashi da kuma Kafur LGAs,” in ji shi.

Kazalika, dakarun tsaro sun ƙaddamar da wani aiki da sanyin safiyar ranar 10 ga watan Afrilun shekarar 2025, a hanyar da ɓarayin daji ke bi a Dutsen Wori gefen hanyar  Dandume zuwa Kandamba, da ke wajen garin Dandume a kan iyaka da ƙananan hukumomin Faskari da Sabuwa.

Aikin da aka aiwatar da misali ƙarfe 3:45 na dare ya yi silar kashe ɓarayi shida ciki har da shugabansu, yayin da sauran ɓarayi suka tsere da raunukan bindiga.

 Bayanai sun nuna cewa dakarun sun ƙwace mashina bakwai yayin da saura huɗu suka tsere cikin daji. An bi sawun ɓarayin ne daga dabarsu da ke Maigora/Doroyi cikin ƙaramar hukumar Faskari.

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#