Sport
Dollar
38,1334
0.13 %Euro
43,5762
1.26 %Gram Gold
4.057,4800
2.59 %Quarter Gold
6.713,0700
3.09 %Silver
40,4500
2.17 %Tawagar ta Super Eagles ce ta tabbatar da mutuwar tsohon ɗan wasan na Nijeriyar ranar Asabar a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X.
Tsohon kocin tawagar ƙwallon ƙafar Nijeriya ta Super Eagles, Christian Chukwu, ya mutu.
Tawagar ta Super Eagles ce ta tabbatar da mutuwar tsohon ɗan wasan na Nijeriyar ranar Asabar a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X.
Sanarwar ta ambato shugaban hukumar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya, Dr Mohammed Sanusi, yana alhinin mutuwar tsohon kyaftin ɗin Nijeriyar wanda ya jagoranci tawagar Eagles da ta lashe gasar cin kofin ƙwallon ƙafa ta Afirka a shekarar 1980.
“Mun rasa gwarzo. Chukwu shi ne asalin namiji mai ƙwari, mai sadauƙar da kai kuma shugaba mai mayar da hankali kan aiki a ciki da wajen filin wasa,” kamar yadda sanarwar ta ambato Sanusi yana cewa.
Sanarwar ta ƙara da cewa Chukwu na cikin tawagar ƙwallon ƙafar Nijeriya da ta samu lambar yabo ta tagulla a gasar ƙwallon ƙafar Afirka ta shekarar 1976 da kuma ta shekarar 1978 waɗanda aka buga a Ethiopia da kuma Ghana, kafin ya jagoranci tawagar zuwa nasarar ɗaukar kofi a a Nijeriya a shekarar 1980.
An karrama shi da lambar yabo ta ɗan wasan da ya fi iya murza leda a gasar ta shekarar 1980.
Chukwu, wanda aka haifa a ranar 4 ta watan Janairun shekarar 1951, ya yi aiki a matsayin coci a kulob ɗin da ya yi wasa na Rangers International kana ya yi aikin koci a tawagar ƙwallon ƙafa ta Kenya (Hamabee Stars).
A shekarar 2004 ya jagoranci tawagar Super Eagles zuwa gasar cin kofin Afirka da aka yi a Tunisia.
“Mutuwarsa tana zuwa ne kwana 20 bayan an cika shekara 45 da Nijeriya ta lashe gasar cin kofin Afirka ta shekarar 1980,” in ji sanarwar.
Cikin ‘yan wasan tawagar da ta lashe kofin na shekarar 1980 da suka riga mu gidan gaskiya akwai Best Ogedegbe da Moses Effiong da Okechukwu Isima da Tunde Bamidele da Atugbu da Mudashiru Lawal da kuma Martins Eyo, in ji sanarwar ta Super Eagles..
Comments
No comments Yet
Comment