Dollar

38,1588

0.3 %

Euro

43,6101

1.61 %

Gram Gold

3.958,7400

2.25 %

Quarter Gold

6.529,2600

2.67 %

Silver

39,4700

3.6 %

Hukumomi sun ce shirin na da burin inganta lafiyar jami’ai ta hanyar ayyukan motsa jiki ba ƙaƙƙautawa da kuma gwaje-gwaje na lafiya.

‘Yan sandan Afirka ta Kudu masu ‘ƙiba’ za su shiga tsarin rage teɓa

Hukumar ‘yan sanda Afirka ta Kudu (SAPS) ta yi shelar ƙaddamar da wani shiri na lafiya da motsa jiki ga ‘yan sandan da ake ganin ba za su iya aiki da kyau ba.

An bayyana shirin ne a rana ta ƙarshe ta taron aikin ‘yan sanda, wanda aka yi tsakanin ranar 9 zuwa 11 ta watan Afrilu, inda manyan jami’an ‘yan sanda suka tattauna kan dabarun yaƙar laifuka masu zurfi  yayin da ƙasar ke fama da ƙaruwar aikata laifuka. 

Manjo-Janar Busi Temba daga ɓangaren kula da ma’aikata na SAPS ya yi cikakken bayani game da shirin da zai gano jami’ai “masu ƙiba” domin a saka su cikin shirye-shiryen lafiya, kamar yadda kafar watsa labaran ƙasar SABC ta ruwaito.

"Za mu gano waɗannan jami’an ne tare da abokan aikinmu na shirin lafiya domin a saka waɗannan jami’an cikin shirin inda za su yi ayyuka, kuma bayan shirin, za a yi gwaji kafin da kuma bayan shirin."

Gwajin lafiya

Temba ya ƙara da cewa shirin na son inganta lafiyar gangan jikin jami’ai ta hanyar ayyukan motsa jiki ba ƙaƙƙautawa da kuma gwaje-gwajen lafiya.

Taron na zuwa ne a bayan hukumar aikin ‘yan sanda ta SAPS ta sake alƙalluman laifuka da aka yi tsakanin watan Okoba zuwa watan Disambar shekarar 2024.

Alƙalluman sun bayyan cewa an aikata laifukan kisan kai 7,710 da laifuka mai alaƙa da jima’i 14,973 da laifuka 12,447 na farmaƙi da niyyar rauni da kuma laifukan fashi mai tsanani 35,030 a cikin lokacin.

Afirka ta Kudu ta shafe gwamman shekaru tana fama da yawan laifuka, lamarin da ke silar salwantar rayuka da yawa, ciki har da na mashahuran mutane da kuma ‘yan wasa.

Yaƙi da laifuka

A wani jawabi ga manema labarai a taron, kwamishin ‘yan sandan lardin Gauteng Tommy Mthombeni ya yi bayanin samun nasarar wargaza wasu ƙungiyoyin masu aikaita laifuka.

Ya bayyana cewa fiye da mutum 100 cikin mutum 400 da ake zargi da hannu da aikata miyagun laifuka irin su fashi da makami da garkuwa da mutane da kuma satar mota an kama su ko kuma an “kakkaɓe su.”

Da yake magana game da matsalolin da ke lardin Western Cape, musamman a birnin Cape Town, kwamishin ‘yan sandan Thembisile Patekile ya jaddada buƙatar gaggawa ta inganta kayayyakin aikin fasaha domin yaƙar laifuka yadda ya kamata.

"Muna godiya cewa birin Cape Town na da kamarorin CCTV a wurare da yawa da kuma wurare masu cinkoso irin su Manenberg da Nyanga da kuma  ire-iren su. Amma za mu so ƙarin haka … domin kashi 65 zuwa 75 cikin 100 na laifukanmu na faruwa ne cikin Cape Town, musamman a yankin unguwar Cape Flats."

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#