Sport
Dollar
38,1588
0.3 %Euro
43,6101
1.61 %Gram Gold
3.958,7400
2.25 %Quarter Gold
6.529,2600
2.67 %Silver
39,4700
3.6 %An yi maraba da wannan mataki a yankunan ƙasashen Hausa da dama, musamman a arewacin Nijeriya.
Gwamnatin Nijar ta amince da harshen Hausa a matsayin yaren ƙasa a madadin Faransanci, a wani ƙarin matakin rabuwa da Faransa, wadda ta yi wa ƙasar mulkin mallaka.
Tun bayan kifar da gwmanatin farar hula ta shugaba Mohamed bazoum a watan Yulin 2023, alakar gwamnatin Nijar da Faransa ta yi tsami, inda suka kori sojojin Faransa da sake sunayen tituna da wuraren tarihi da ke ɗauke da sunayen Faransawa.
“Yaren kasa shi ne Hausa” kuma “yarukan ayyuka su ne Turancin Ingilishi da na Faranshi”, in ji wata sanarwa ta musamman da aka buga a mujallar gwamnati ta ranar 31 ga Maris.
Nijar da Mali da Burkina Faso - duk kasashen da Faransa ta yi wa mulkin mallaka - sun fice daga Kungiyar Ƙasashe Rainon Faransa (OIF), wata ƙungiya mai kama da ta ƙasashe rainon Ingila, wato Commenwealth, da aka kafa bayan mulkin mallaka .
Hausa ne yaren da aka fi magana da shi a ƙasar mai yawan mutane da suka kai miliyan 26, musamman a Zinder da Maraɗi da ke tsakiya maso kudanci, da kuma a Tahoua a yammacin Nijar.
Kimanin kashi 13 na jama’ar Nijar na magana da yaren Faranshi, ko kuma dai sama da mutum miliyan uku.
Sauran yarukan ƙasar sun haɗa da Zarma da Songhay da Fula da Kanuri da Gourmanche da Larabci, a yanzu sun zama “yarukan da ake magan da su a Nijar”, in ji sanarwar da aka fitar.
Matakin wani ɓangare ne na sakamakon Babban Taron Ƙasa da aka gudanar a watan Fabrairu ne, wanda ya bayar da wa’adin shekaru biyar ga mulkin sojojin da Janaral Abdourahamane Tiani ke jagoranta
Comments
No comments Yet
Comment