Sport
Dollar
38,1373
0.02 %Euro
43,6701
-0.15 %Gram Gold
4.081,8100
-0.41 %Quarter Gold
6.731,9300
0 %Silver
39,8500
-0.83 %“Abin baƙin ciki ne hare-haren baya bayan nan da aka kai wa jami’an tsaro a Wajirko, da Sabon Gari a karamar hukumar Damboa, da Wulgo a Gamboru Ngala, da Izge a ƙaramar hukumar Gwoza da ma wasu yankunan inda aka samu asarar rayukan fararen hula.
Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya bayyana cewar sabbin hare-haren Boko Haram da garkuwa da mutane a garuruwa kusan a kowace rana ba tare da tunkarar ‘yan ta’addar ba na nuna cewa ana cin jihar Borno da yaƙi.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata a yayin gudanar da wani Taron Tsaro na Musamman da ya jagoranci gudanarwa a babban birnin jihar, Maiduguri.
Ya ce gwamnatinsa na taimaka wa sojojin Nijeriya sosai a yaƙin da suke yi da ‘yan ta’addar Boko Haram da sauran ‘yan ta’adda wanda ya kawo ɗan zaman lafiyar da ake da shi a jihar a shekaru ukun da suka gabata.
Hare-Hare na fatattakar cibiyoyin tsaro
Gidan talabijin na Channels ya rawaito gwamna Zulum ya bayyana damuwa game da yadda hare-haren baya bayan nan ke fatattakar cibiyoyin jami’an tsaro a Wajirko, da Sabon Gari a karamar hukumar Damboa, da Wulgo a Gamboru Ngala, da Izge a ƙaramar hukumar Gwoza da ma wasu yankunan, inda aka samu asarar rayukan fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba da ma jami’an tsaro.
Zulum ya ƙara da cewa wannan hali da aka tsinci kai a ciki na sanya matukar damuwa da bayyana koma baya a jihar Borno da ma yankin arewa maso-gabashin Nijeriya.
Gwamnatin Nijeriya na kokari
Gwamnan na jihar Borno Zulum ya yaba wa gwamnatin tarayyar Nijeriya ƙarƙashin shugabancin Bola Tinubu da hukumomin tsaro, saboda taimako da goyon baya ba ƙaƙƙautawa da suke bayarwa wajen yaƙi da Boko Haram.
Ya bayyana cewa akwai buƙatar kara ƙaimi da zage damtse ta hanyar samar da kayan aiki na zamani ga sojoji, don magance duk wasu sabbin hare-hare da ke damun yankin Sahel na jihar Borno, wanda ke da iyakar ƙasa da ƙasa da ƙasashen Afirka uku, Chadi, da Nijar da Kamaru.
Ya ce “A yayin da na ke bayani ga wannan muhimmin taro a yanzu haka, abin takaici ne yadda sabbin hare-haren Boko Haram da garkuwa da mutane a garuruwa da dama ke afkuwa kusan a kowace rana ba tare da an kalubalance ba, hakan na nufin cewa ana cin Borno da yaki.”
Gwamnatina na taimaka wa sha’anin samar da tsaro
Zulum ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar Borno da yake jagoranta na tallafa wa sojoji da sauran hukumomin tsaro wajen yaki da Boko Haram da sauran ‘yan ta’adda wanda ya bayar da damar samun ɗan zaman lafiya a shekaru ukun da suka gabata.
“Abin bakin ciki ne a ce hare-haren baya bayan nan da aka kai wa jami’an tsaro a Wajirko, da Sabon Gari a karamar hukumar Damboa, da Wulgo a Gamboru Ngala, da Izge a ƙaramar hukumar Gwoza da ma wasu yankunan inda aka samu asarar rayukan fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba da ma jami’an tsaro,.” in ji gwamna Zulum.
Gwamna Zulum ya buƙaci da a ɗauki ƙarin matakan daƙile sake ganin hare-haren da manufar kawo karshen ta’addanci a jihar, da arewa maso-gabas da ma Nijeriya baki ɗaya.
Har yanzu wasu yankunan Borno na hannun ‘yan ta’adda
Da yake bayani a madadin shugabannin gargajiya, Shehun Borno Alh Dr Abubakar Garbai Al-Amin El-Kanemi ya yaba wa hukumomin tsaro da ke yaki da ta’addanci a yankin.
Ya bayyana takaicinsa kan yadda har yanzu ƙananan hukumomin Guzamala, da Marte, da Abbadam da wani yanki na ƙaramar hukumar Mobbar ke ci gaba da kasancewa a ƙarkashin ikon ‘yan ta’addar Boko Haram.
Ya ce “mafi yawan wadannan yankuna ba su da shugabanci”.
Shehun Borno ya kuma yi kira ga gwamnatin Nijeriya da ta gyara hanyoyin jihar da suka haɗa da na Biu zuwa Damboa zuwa Maiduguri, da hanyar Maiduguri zuwa Dikwa zuwa Ngala, da hanyar Maiduguri zuwa Monguno zuwa Kukawa, da kuma hanyar Biu zuwa Damaturu.
Taron ya samu halartar Babban Kwamandan Soji na Runduna ta 7 Janar Abubakar Haruna, da Kwamandojin Soji, da Kwamishin ‘Yan Sanda, da shugabannin hukumomin tsaro, da Shehun Borno Alh Dr Abubakar Garbai Al-Amin El-Kanemi, da Shehun Bama, da Sarakun Biu, da Uba, da Askira, da Gwoza inda Shehun Dikwa.
Comments
No comments Yet
Comment