Sport
Dollar
38,2623
0.12 %Euro
43,8041
-0.64 %Gram Gold
4.174,6500
-0.83 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Sanarwar ta bayyana cewa taron zai kuma fayyace sauran batutuwa masu muhimmanci ga yankin.
Kwamitin Ministoci na Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Afirka ta Yamma, ECOWAS zai yi wani taro na musamman don tattaunawa a kan janyewar Burkina Faso da Mali da Nijar da cikin ƙungiyar.
Babban jami’in sadarwa da wata labarai na ECOWAS, Joel Ahofodji a wata sanarwa ya ce muhimman batutuwan da za a tattauna sun haɗa da yadda tsarin janyewar zai kasance da kuma tasirin hakan kan cibiyoyin ECOWAS da hukumominta da ke aiki a ƙasashen uku.
Sanarwar ta bayyana cewa taron zai kuma fayyace sauran batutuwa masu muhimmanci ga yankin.
ECOWAS na taron cika shekara 50 da kafuwa
A yau Talata 22 ga watan Afrilun 2025 ne kuma ƙungiyar ta ECOWAS za ta kaddamar da bikin cikarta shekara 50 da kafuwa a birnin Accra na Ghana.
The programme of activities was validated by the ECOWAS Administrative and Financial Committee during a virtual meeting in February 2025.
Originally comprised of 15 nations, ECOWAS welcomed Cabo Verde in 1977, while Mauritania withdrew in 2000, signing an association agreement in 2017.
Taron yana nuna fara gudanar da bukukuwan tunawa da kafa Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Afrika ta Yamma, wadda aka kafa shekaru 50 da suka gabata a ranar 28 ga watan Mayun shekarar 1975 a birnin Lagos na Nijeriya.
Ana sa ran shugabannin kasashe mambobin za su halarci taron kaddamar da shirin bikin.
Daga cikin wadanda suka fara isa Ghana don halartar taron akwai Mista Muhammed B. S. Jallow, Mataimakin Shugaban Ƙasar Gambia.
Za a gudanar da bukukuwa a fadin kasashe mambobin kungiyar a cikin shekarar nan dukkanta, kamar yadda taron shugabannin kasashen kungiyar ECOWAS ya ba da shawara.
Kwamitin Gudanarwa da Kudi na ECOWAS ne ya tabbatar da shirin a yayin taron da aka yi a watan Fabrairun 2025.
Asali ƙungiyar ECOWAS ta ƙunshi ƙasashe 15 ne, amma daga baya a shejarar 1977 ta yi maraba da Cabo Verde, yayin da Mauritania ta fice a shekarar 2000, inda ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya a shekarar 2017.
Comments
No comments Yet
Comment