Dollar

38,2567

0.07 %

Euro

44,0756

-0.13 %

Gram Gold

1.157,1500

-2.11 %

Quarter Gold

6.947,4100

0 %

Silver

40,2000

0.07 %

Amurka tana shirin rufe ofisoshin jakadancinta a Eritrea, Gambia, Kudancin Sudan, Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo, Lesotho, da kuma Jamhuriyar Afirka Ta Tsakiya.

Gwamnatin Trump tana shirin rufe ofisoshin jakadancinta a faɗin Afirka

Amurka tana rage ayyukan ci-gaba da diflomasiyya a Afirka sosai, wanda hakan ya haifar da damuwa game da makomar kiwon lafiya da ilimi, da ci-gaban tattalin arziki a yankin.

A karkashin gwamnatin Trump, wata doka da aka fallasa ta bayyana shirin sake fasalin ayyukan Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka a Afirka da kuma rage shirye-shiryen Hukumar Raya Kasa ta Amurka (USAID) sosai.

Amurka, wadda a tarihi ta kasance tana da ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi yawan ofisoshin jakadanci a Afirka—wanda ƙasar China ce kawai ta fi ta—na shirin rufe ofisoshin jakadanci a kasashen Eritrea, Gambiya, Sudan ta Kudu, Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, Lesotho, da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, tare da ofisoshin jakadanci a Kamaru da Afirka ta Kudu.

Shirye-shiryen da aka tsara sun kuma nuna cewa za a rushe sassan Ma’aikatar Harkokin Wajen da ke kula da harkokin Afirka da inganta dimokuraɗiyya da kare haƙƙin ɗan’adam, manufofin ‘yan gudun hijira, daidaito tsakanin jinsi, da batutuwan yanayi.

Dakatar da tallafi

A watan Janairu, Washington ta dakatar da tallafin kasashen waje na USAID na tsawon kwanaki 90.

Wannan ragewar ta yi matukar shafar shirye-shiryen kiwon lafiya, ilimi, da ci-gaba a yankin kudu da hamadar Saharar Afirka da ba da magungunan HIV/AIDS da rigakafin zazzabin cizon sauro, kula da lafiyar uwa, da taimakon noma.

Kasashe kamar Kenya, Uganda, da Nijeriya sun tilasta dakatarwa ko rage wasu shirye-shiryen da ke ceton rayuka.

Hankalin USAID yanzu ya karkata ne zuwa ga wasu ƙasashe kaɗan da ake kira “ƙasashe masu muhimmanci,” inda ake rage kasancewarta a sauran wurare.

A cewar shafin bayanan Taimakon Kasashen Waje na Amurka, wasu kasashen Afirka da suka hada da Equatorial Guinea, Eritrea, Gabon, Guinea-Bissau, Mauritius, Sao Tome da Principe, da Seychelles, ba su samu tallafi ba a wannan shekarar.

Wasu kuma, kamar Cape Verde, Comoros, da Gambiya, sun samu tallafi kadan kawai.

Warware matsala a cikin gida

A martani kan hakan, wasu gwamnatocin Afirka suna neman hanyoyin warware matsalar a cikin gida. Nijeriya ta ware dala miliyan 200 don cike gibin tallafin kiwon lafiya.

Duk da haka, yawancin sauran kasashe suna fuskantar kalubale kamar cin hanci da rashin ingantaccen shugabanci, wanda ke sa ake shan wahala wajen ganin ɗorewar irin wadannan ƙoƙari.

Masana sun yi gargadi cewa sai dai idan kasashen Afirka sun fadada abokan hulɗarsu na kasa da kasa kuma suka yi amfani da albarkatun cikin gida yadda ya kamata, idan ba haka ba hannun agogo zai iya komawa baya kan ci gaban da aka samu a kiwon lafiya.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#