Sport
Dollar
38,1488
0.05 %Euro
43,6359
-0.27 %Gram Gold
4.088,5500
-0.25 %Quarter Gold
6.731,9300
0 %Silver
39,9400
-0.6 %Ministan harkokin wajen Nijeriya Yusuf Tuggar ya ce hukumomin Saudiyya sun ƙaryata bayanan da ke nuna cewa an sanya Nijeriya cikin jerin sunayen ƙasashen da aka haramta wa shiga ƙasar.
Ma'aikatar harkokin wajen Nijeriya ta bayyana cewa ƙasar ba ta cikin ƙasashen da ke fuskantar matakin haramcin shiga Saudiyya daga ranar 13 ga watan Afrilu kamar yadda wasu rahotoni suka yi iƙirari.
Ministan harkokin wajen Nijeriya, Yusuf Tuggar ne ya bayyana hakan ta bakin mai taimaka masa na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Alkasim Abdulkadir.
Ministan ya ce gwamnatin Saudiyya a hukumance ta ƙaryata bayanan da ke nuna cewa an sanya Nijeriya cikin jerin sunayen ƙasashen da aka haramta wa shiga ƙasar.
Ya ce babu ƙamshin gaskiya a sanarwar da ta sanya ƙasashen Nijeriya, da Masar, da Indiya, da Pakistan da sauran su a matsayin waɗanda gwamnatin Saudiyya ta haramta wa shiga ƙasar don yin Umrah har zuwa bayan aikin hajji.
“Cibiyar yawon buɗe ido ta Saudiyya ta tabbatar da cewa babu makamancin wannan umarni, ƙa’idojin tafiya a halin yanzu sun shafi aikin Hajji ne kawai.
"Don ƙarin haske, haramcin da ƙasar Saudiyya ta sanya ya shafi waɗanda suke riƙe da bizar yawon buɗe ido a lokacin aikin Hajji," in ji sanarwar.
Masu riƙe da bizar yawon buɗe ido ba za su iya yin aikin Hajji ba, ko shiga ko kuma zama a Makka tsakanin 29 ga watan Afrilu zuwa 11 ga Yuni (01thul Quda zuwa 14thul Hijjah 1446H).
"Bizar aikin Hajji ce kawai za ta bai wa mutum dama ko izinin shiga cikin mahajjata a wannan lokacin," in ji ministan.
Tuggar ya shawarci jama'a da su yi watsi da bayanan da ke yawo a kafofin sada zumunta, kana su nemi duk wani ƙarin haske kan batutuwan da suka shafi tafiye-tafiye ta hanyar hukumomi kafin ɗaukar mataki.
"Yaɗa bayanan da ba a tantance su ba yana haifar da ruɗani kuma yana iya shafar shirye-shirye na tafiye-tafiye," in ji shi.
Comments
No comments Yet
Comment