Dollar

38,1137

0.18 %

Euro

42,0543

-0.85 %

Gram Gold

3.708,4600

-2.33 %

Quarter Gold

6.293,2300

-0.18 %

Silver

36,1600

-6.93 %

Myanmar na fuskantar rugujewar gine-gine da yawa bayan girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 7.7 ta afka wa ƙasar da ke kudancin Asiya, kuma an ayyana dokar ta-ɓaci a yankuna shida na ƙasar.

Mutanen da suka mutu a girgizar ƙasar Myanmar sun zarta 1,000

Yawan mutanen da suka mutu daga mummunar girgizar ƙasar da ta afka wa Myanmar ya ɗara 1,000, kamar yadda rundunar sojin da ke mulkin ƙasar ta bayyana ranar Asabar, inda fiye da mutum 2,000 suka jikkata.

Wata sanarwa da hukumar watsa labaran masu mulkin ƙasar ta fitar ta tabbatar cewa mutum 1,002 sun mutu a girgizar ƙasar ranar Juma’a mai ƙarfin maki 7.7 inda mutum 2,376 suka jikkata.

Girgizar ƙasar ta afka wa arewa maso yammacin birnin Sagaing da ke tsakiyar Myanmar, lamarin da ya janyo rugujewar gine-gine da yawa a sassan ƙasar.

An ayyana dokar ta-ɓaci a larduna shida na ƙasar, ciki har da Mandalay, birni mafi girma a ƙasar, wanda ke kusa da wanda girgizar ƙasar ta afkawa inda aka ga rugujewar abubuwa da yawa.

Wata tawagar ceto ta 'China ta iso ranar Asabar yayin da Rasha da Amurka suka yi tayin taimako a bala’in da ya shafi Thailand ma.

Ana sa ran yawan waɗanda suka mutu zai ƙaru

Shugaban sojojin da ke mulkin ƙasar, Janar Min Aung Hlaing, ya yi gargadi ranar Juma’a game da ƙara samun mace-mace da rauni yayin da ya gayyaci “ko wace ƙasa” ta bayar da taimako ko kuma ta ba da kyaututtuka.

Labari na baya bayan nan da aka samu game da yawan mace-mace ya ɗara 150, kuma sabon labarin yawan mace-mace ya nuna ƙari mai yawa da ya ɗara mutuwar mutum 500.

Amma sadarwa na fuskantar tangarɗa, kuma kawo yanzu gaskiyar yawan bala’in bai bayyana ba gabaɗaya, saboda haka akwai yiwuwar yawan mace-macen zai ƙaru sosai.

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#