Sport
Dollar
38,0186
0.08 %Euro
41,8666
0.79 %Gram Gold
3.665,5300
0.67 %Quarter Gold
6.187,2600
0 %Silver
36,8200
0.12 %Fitaccen ɗan wasan tsakiya na Manchester City wanda ɗan asalin Belgium ne, ya ce zai bar ƙungiyar a ƙarshen kakar bana.
Ɗan wasan ƙwallon ƙafa ɗan asalin Belgium, Kevin De Bruyne, ya sanar da cewa zai bar Manchester City ta Ingila a ƙarshen kakar bana.
A cikin wata sanarwa da ya wallafa a dandalin sada zumunta na X, De Bruyne mai shekaru 33 ya tabbatar da cewa waɗannan su ne watanninsa na ƙarshe a matsayin ɗan wasan Manchester City.
De Bruyne ya je Manchester City a shekarar 2015 daga Wolfsburg, inda ya lashe duka manyan gasar ƙwallon ƙafa tare da ƙungiyar ta City, ciki har da gasar Firimiya ta Ingila da gasar Zakarun Turai.
Kwantiraginsa a City za ta ƙare a ƙarshen Yunin bana, amma har yanzu ba a tabbatar ko zai buga wa City ba a wasannin da za ta buga daga 14 ga Yuni zuwa 13 ga Yuli.
"Kowane labari yana zuwa ƙarshe, amma lallai wannan ya kasance babi mafi kyau a gare ni," a cewar Bruyne. "Mun mori waɗannan lokutan tare har zuwa ƙarshe”.
Ɗan wasan wanda ɗan Belgium ne ya buga wasanni 280 a gasar Firimiya, kuma ya ci ƙwallaye 70 da tallafin ƙwallaye 118. Hakan ya sa shi yake biye da Ryan Giggs tsohon ɗan wasan Manchester United, wanda yake riƙe da kambun wanda ya fi ba da tallafin cin ƙwallo a tarihin Firimiya, da ƙwallaye 162.
Comments
No comments Yet
Comment