Sport
Dollar
38,0077
0.2 %Euro
41,8399
0.52 %Gram Gold
3.643,5900
0.18 %Quarter Gold
6.191,9000
0 %Silver
36,2900
-0.27 %Sufeto Janar na ‘yan sandan Nijeriya ya janye gayyatar da ya yi Sarki Sanusi na Kano zuwa Abuja amsa tambayoyi
Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta sanar da cewa ta janye gayyatar da ta yi wa Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II zuwa hedikwatarta da ke Abuja don amsa tambayoyi kan abubuwan da suka faru a wajen Hawan Sallah ranar 30 ga watan Maris din da ya gabata.
Tun da fari a ranar Asabar ne Sufeto Janar na rundunar ‘yan sandan ya aika wa Sarki Sanusi takatardar gayyata don ya amsa tambayoyi a kan “tashe-tashen hankulan” da a cewar rundunar sun faru a lokacin bukukuwan sallah, sakamakon fitar sarkin Sallar Idi, wanda rundunar ta ce tun da fari ta haramta yin Hawan Sallah.
A sabuwar sanarwarta da ta wallafa a shafin X a ranar Lahadi, rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta ce “da farko dai an yi wannan gayyata ne domin bai wa Alhaji Sanusi damar ba da bayani kan abubuwan da suka haifar da tabarbarewar doka da oda a jihar.”
Sanarwar ta ƙara da cewa “To sai dai kuma sakamakon shawarwarin masu ruwa da tsaki da ake mutuntawa da suka yi daidai da ƙudurin Sufeto-Janar na ‘yan sanda na tabbatar da cewa ba a siyasantar da ayyukan ‘yan sanda ba ko kuma a yi musu mummunar fassara, sufeton ya ba da umarnin a janye gayyatar.”
A maimakon haka, rundunar ta ce ta umarci jami’an sashen leƙen asiri na rundunar FID bisa umarnin Sufeto-Janar da su je Kano domin samun bayani daga baki Sarki Sanusin.
Gabanin bikin Sallah, ‘yan sanda sun ce wasu bayanan sirri da suka samu sun nuna cewa sarakunan biyu da ke rikici a jihar Kano – Sarki Sanusi da Sarki Aminu na shirin gudanar da bukukuwan Hawan Sallah daban-daban.
Bikin Hawan Sallah al'ada ce da aka dade ana yi wadda ta ƙunshi Sarki da Hakimansa su yi hawa dawakai a cikin birni tare da jama'arsu.
“Domin hana faruwar tashin hankali, Sufeto-Janar na ‘yan sanda Kayode Adeolu Egbetokun, ya tura DIG na shiyyar Arewa maso Yamma wanda kuma ya kasance mataimakin sufeto-janar na ‘yan sanda mai kula da sashen binciken manyan laifuka na rundunar, DIG Sadiq Abubakar, domin tattaunawa da sarakunan Kano biyu,” in ji ‘yan sandan.
Sun ƙara da cewa tun da fari “an dai amince cewa ba za a gudanar da wani biki na hawa ba don kiyaye zaman lafiya da kare lafiyar al’umma kuma babu wani daga cikin sarakunan da ake takaddama a kai da zai hau doki a ranar Sallah.
“Duk da wannan yarjejeniya, Alhaji Sanusi wanda ya halarci Sallar Idi a cikin motarsa, ya yanke shawarar hawan doki bayan Sallar Idi a ranar Sallah tare da rakiyar ’yan bijilante na yankin.
“Hakan ya haifar da wata arangama da matasan unguwar suka yi, lamarin da ya yi sanadin mutuwar wani Usman Sagiru, tare da jikkata wasu da dama. Lamarin da a baya rundunar ta yi gargadi a kai, kuma ta yi niyyar kaucewa ta hanyar sakonnin da aka fitar tun da farko ga Alhaji Sanusi da Alhaji Ado Bayero.
“Rundunar ‘yan sandan Nijeriya a karkashin jagorancin babban sufeton ‘yan sandan kasar na ci gaba da jajircewa wajen gudanar da ayyukanta na binciken laifuka tare da kwarewa mafi girma da suka hada da binciken wannan lamari.”
A ƙarshe rundunar ta ce duk mutanen da aka samu da laifi a karshe za a gurfanar da su gaban kotu.
“Don haka, an kama wasu da ake tsare da su inda aka gayyace su zuwa wurin Alhaji Sanusi.”
Comments
No comments Yet
Comment