Sport
Dollar
38,0100
0.07 %Euro
41,6259
0.36 %Gram Gold
3.645,1100
0.11 %Quarter Gold
6.191,9000
0.07 %Silver
36,5500
-0.63 %Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta ce zanga-zangar da wata ƙungiya mai suna “Take It Back” ta shirya tana zuwa ne a lokacin da bai dace a yi zanga-zanga a ƙasar ba.
Rundunar ‘yan sandan Nijeriya ta gargaɗi masu shirin yin zanga-zanga ranar Litinin 7 ga watan Afrilu a faɗin ƙasar su sake tunani domin a ranar ce ‘yan sandan ƙasar suke bukukuwa domin nuna gudunmawar da suka bayar don ci-gaban Nijeriya.
Ta ce zanga-zangar da wata ƙungiya mai suna “Take It Back” ta shirya tana zuwa ne a lokacin da bai dace a yi zanga-zanga a ƙasar ba.
Wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan ƙasar, Olumuyiwa Adejobi, ya fitar ta ce rundunar ba ta adawa da ‘yancin ‘yan ƙasar na taruwa da yin gangami da kundin tsarin mulkin Nijeriya ya ba su.
Sai dai kuma sanarwar ta ce rundunar na fargaba game da burin waɗanda suka shirya yin zanga-zangar rana ɗaya da ranar da aka ware domin yaba wa irin jajircewa da sadaukar da kai na ‘yan sandan Nijeriya.
“Bisa ga ingatattun ɗabi’un da ƙasashen duniya ke bi wajen yabawa da nasarorin ‘yan sandansu, gwamnatin Nijeriya ta ɗauki matakin ayyana ranar 7 ga watan Afrilu a matsayin ranar ‘yan sandan Nijeriya,” in ji sanarwar.
Sanarwar ta ƙara da cewa bikin zai samu halartar baƙi daga ciki da wajen ƙasar daga fannoni daban-daban, ciki har da sufeto janar na ‘yan sandan ƙasashen ƙetare da kuma jami’an diflomasiyya.
“Dalilin gudanar da zanga-zanga a irin wannan ranar abin dubawa ne kuma a iya cewa wani mataki ne na ɓata sunan ‘yan sandan Nijeriya da ƙasar ma baki ɗaya,” in ji sanarwar.
“Saboda haka rundunar ‘yan sandan Nijeriya tana bai wa waɗanda suka shirya wannan zanga-zangar shawarar janyeta saboda lokacin bai dace da ita ba kuma tana da manufar aikata ɓarna,” in ji Olumuyiwa.
Comments
No comments Yet
Comment