Dollar

38,4211

0.21 %

Euro

43,6212

-0.35 %

Gram Gold

4.048,7700

-1.96 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Gwamnan lardin da ‘yan tawaye suka naɗa ya ɗora alhaƙin ruftawar mahaƙar ma’adinkan yadda ake gina ramukan haƙar zinare ba tare da tsari ko kula ba—lamarin da ke yawan janyo hatsari a wuraren haƙar ma’adinai a gabashin Jamhuriyar Dimokraɗiyyar Kongo.

An samu mace-mace bayan ruftawar mahaƙar ma’adinai a gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo

Aƙalla mutum 10 sun mutu a ruftawar mahaƙar ma’adinai a gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo, in ji gwamnan lardin South Kivu da ‘yan tawaye suka naɗa.

Douglas Dunia Masumbuko, gwamnan South Kivu da ƙungiyar M23 ta naɗa, ya shaida wa Reuters ranar Alhamis cewa adadin waɗanda suka mutu a mahaƙar ma’adinan Luhihi ya kai mutum 10 kuma zai iya ƙaruwa saboda yawan waɗanda suka ji rauni a wurin."

Ya ɗora alhaƙin hatsarin kan "gina mahaƙar zinare ba tare da tsari ko kula mai kyau ba " a yankin.

‘Yan tawayen M23 sun karɓe iko da birane biyu mafi girma a gabashin Kongo tun watan Janairu a lokacin da rikicin da aka daɗe ana yi tun lokacin da kisan ƙaren dangin Rwanda na shekarar 1994 ya fantsama cikin Kongo da kuma neman iko kan ma’adinan Kongo ya tsananta.

Gwamnatin Kongo da kuma ƙungiyar M23 sun yi alƙawari a wata sanarwar da aka fitar ranar Laraba bayan tattaunawa a Qatarcewa za su yi aiki tare domin tabbatar da zaman lafiya, lamarin da ya ƙara fatan kawo ƙarshen tashin hankali na baya bayan nan.

Ana yawan samun haɗɗuran mahaƙar ma’adinai a babbar ƙasar ta tsakiyar Afirka , musamman a ƙananan mahaƙar ma’adinai.

Gwamna Jean-Jacques Purusi, wanda a baya ya kasance gwamnan lardin South Kivu kafin M23 ta karɓe iko da lardin, ya tabbatar da cewa an samu ruftawar ramin haƙar ma’adinan, amma bai ba da adadin waɗanda suka mutu ba.

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#