Sport
Dollar
38,4292
0.2 %Euro
43,8350
-0.02 %Gram Gold
4.095,0600
-0.84 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Mai magana da yawun gwamnatin Wilfried Léandre Houngbédji ce an kuma kashe mahara 33 a a karawar da suka yi da sojojin Benin, kuma an samu waɗadanda suka ji raunuka da dama a ɓangarorin biyu.
'Gwamnatin Benin ta tabbatar a ranar Laraba cewa an kashe sojoji 54 a ranar 17 ga Afrilu a hare-hare da ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai suka kai a yankunan arewacin kasar.'
Jaridar La Nouvelle Tribune ta ruwaito cewa mai magana da yawun gwamnati Wilfried Léandre Houngbédji ya aike da ta'aziyya ga iyalan sojojin da suka mutu.
Ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa adadin wadanda suka mutu a cikin Rundunar Tsaro da Tsaron Lafiya, yayin hare-haren ba ɗaruruwa ba ne, saɓanin bayanan da aka ringa yaɗawa a kafafen sada zumunta.
Hare-haren da aka kai wa sojoji a wurarensu a yankin da ke tsakanin Benin da Nijar da Burkina Faso, da kuma yankin mazubar ruwan Koudou.
Houngbédji ya ce an kashe sojoji takwas a mazubar ruwan Koudou da 46 a kan iyakar ƙasashen uku.
Ya jaddada cewa 'wannan ba ya rage girman abin da ya faru.' Bugu da ƙari ga asarar sojoji, Houngbédji ya bayar da rahoton cewa an kashe mahara 33 a a karawar da suka yi da sojojin Benin, kuma an samu waɗadanda suka ji raunuka da dama a ɓangarorin biyu.
Ya jaddada buƙatar ƙarfafa ƙwarewar aikin sojoji, musamman a fannin dabaru da kayan aiki, don magance barazanar ta'addanci.
Houngbédji ya ambato rashin haɗin kai da ƙasashe maƙwabta a matsayin daya daga dalilan ci gaba da hare-haren.
Arewacin Benin ya fuskanci ƙaruwar hare-hare daga ƙungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi da ke da alaƙa da al-Qaeda da Daesh, suna shiga daga ƙasashe maƙwabta da suka haɗa da Burkina Faso da Nijar.
Bisa haka ne gwamnatin Benin ta ƙaddamar da Operation Mirador a watan Janairu na shekarar 2022, inda ta tura sojoji kusan 3,000 da ɗaukar ƙarin 5,000 domin tsaurara tsaro a wuraren da ke cikin haɗari.
Comments
No comments Yet
Comment