Sport
Dollar
38,2909
0.07 %Euro
43,6646
-0.09 %Gram Gold
4.100,3800
-1.45 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%An dakatar da Gertrude Torkornoo daga muƙaminta ne sakamakon wasu koke guda uku da aka gabatar a kanta.
Shugaban Ghana John Dramani Mahama ya dakatar da Alƙaliyar Alƙalan ƙasar Mai Shari’a Gertrude Torkornoo nan-take a karon farko da irin haka ta faru a tarihin ƙasar.
Kazalika shugaban ya bayar da umarni a yi bincike a kanta sakamakon ƙorafe-ƙorafe uku da aka gabatar a kanta waɗanda ba a bayyana ba.
Alƙalan Alƙalan Ghana suna da wa’adin sauka daga muƙaminsu - wato ba za a iya cire su haka kawai ba, idan ba an same su da laifin rashin iya gudanar da aiki da karya doka ba.
A watan jiya ne Mahama ya miƙa ƙorafe-ƙorafe na neman cire Mai Shari’a Torkornoo ga Majalisar Magabata domin ta yi nazari kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya zayyana.
Kamfanin dillancin labaran Ghana ya ruwaito cewa matakin wani ɓangare na soma bin tsarin cire Alƙaliyar Alkalan kamar yadda Layi na 146 na Kundin Tsarin Mulkin Ƙasar na 1992 ya tsara.
An rantsar da Mai Shari’a Torkornoo a matsayin Alƙaliyar Alƙalan Ghana ranar 12 ga watan Yunin shekarar 2023, inda ta maye gurbin Mai Shari’a Kwasi Anin Yeboah, wanda ya yi ritaya a watan Mayu na 2023.
Kafin a naɗa ta kan muƙamin, Mai Shari’a Torkornoo ta yi aiki a matsayin Alƙaliyar Kotun Ƙoli, bayan ta shiga cikin jerin alƙalan kotun a shekarar 2019.
Comments
No comments Yet
Comment