Sport
Dollar
38,4229
0.21 %Euro
43,6816
-0.21 %Gram Gold
4.055,6500
-1.79 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%A ranar Laraba ne Bankin Duniya ya ƙaddamar da mataki na gaba a shirinsa na ƙawance da manyan masu zuba jari na duniya, wanda zai magance matsalolin da ke tarnaƙi ga harkokin zuba jari a duniya.
Shugaban kamfanin Dangote, Aliko Dangote ya karɓi muƙamin da Bankin Duniya ya ba shi a shirin nan na Ƙawancen Bankin Duniya da Masu Zuba Jari na Duniya.
A ranar Laraba ne Bankin Duniyar ya sanar da ƙaddamar da mataki na gaba a shirin nasa na ƙawance da manyan masu zuba jari na duniya, wanda ke mayar da hankali wurin lalubo mafita da magance matsalolin da ke kasancewa tarnaƙi ga harkokin zuba jari a duniya.
A shekarar 2023, Firaministan Canada, Mark Carney, ya jagoranci ƙawancen masu zuba jarin, wanda ya jawo zuba jari na fam tiriliyan ɗaya domin taimaka wa shirin da ake na komawa amfani da makamashi maras gurɓata muhalli a kasuwannin duniya masu tasowa.
A cikin wata sanarwa da ya tabbatar na karɓar muƙamin, Dangote ya jaddada aniyarsa ta samar da ci gaban tattalin arziki mai ɗorewa ta hanyar zuba jari da kamfanoni masu zaman kansu ke jagoranta, inda ya yi nuni da yadda irin waɗannan tsare-tsare za su iya kawo sauyi a kasuwanni masu tasowa.
"Na yi matuƙar farin ciki da amincewa da naɗin da aka yi mani na shirin nan na Ƙawancen Bankin Duniya da Masu Zuba Jari na Duniya, wanda aka samar domin samar da ci gaba ga zuba jari da samar da ayyukan yi a ƙasashe masu tasowa,” kamar yadda Dangote ya bayyana.
Dangoten ya ƙara da cewa, “Wannan damar ta zo daidai da abin da na daɗe ina yi na samar da ci gaba mai ɗorewa da kuma buɗe ƙofa ga ci gaba a ƙasashe masu tasowa. Mun samu ƙwarin gwiwa daga irin ci gaban da manyan ƙasashen Asia huɗu suka samu, waɗanda suka nuna yanayin ƙarfin ƙasashen Afirka huɗu, hakan ya nuna ƙarfin zuba jari da dabara inda suka mayar da hankali kan tattalin arziki.
“A shirye nake na haɗa kai da sauran jagorori domin samar da irin wannan ci gaba a sauran yankuna,” kamar yadda sauran suka tabbatar.
Sauran waɗanda za su yi aiki tare da Dangote a wannan ƙawancen sun haɗa da Shugaban Bayer AG, Bill Anderson da Shugaban Bharti Enterprises, Sunil Bharti Mittal da Shugaban Hyatt Hotels, Mark Hoplamazian.
Comments
No comments Yet
Comment