Dollar

38,4292

0.2 %

Euro

43,8350

-0.02 %

Gram Gold

4.095,0600

-0.84 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Laftanar Janar Olufemi Oluyede ya umarci dakarunsa su kawar da 'yan bindiga na ƙungiyar Mahmuda daga ƙananan hukumomi biyu da suka yi ƙarfi a Jihar Kwara, inda ya ba su wata ɗaya su kammala aikin.

Mahmuda: An umarci sojin Nijeriya su murƙushe sabuwar ƙungiyar masu iƙirarin jihadi daga Jihar Kwara

Babban Hafsan Sojojin Ƙasa na Nijeriya ya bai wa dakarunsu wa’adin wata ɗaya domin su kawar da sabuwar ƙungiyar ‘yan bindiga mai suna Mahmuda da ta ɓulla a Jihar Kwara ta tsakiyar ƙasar.

Laftanar Janar Olufemi Oluyede ya bayar da umarnin ne yayin da yake jawabi ga dakarunsa a barikin Sobi na Ilorin, babban birnin jihar ta Kwara.

Ƙungiyar Mahmuda, wadda ke ikirarin jihadi, ta addabi jama’a a wasu yankuna na ƙananan hukumomin Baruten da Kaiama na Jihar ta Kwara.

Ya ce ba zai bari wata ƙungiya da ta yi kama da ƙungiyar Boko Haram ta sake samun wurin zama a kowane yanki na Nijeriya ba.

“Don haka, tun da yanzu kuna nan wurin kuma na san za ku iya tabbatar da ganin waɗannan mutane sun bar mana wannan wuri. Idan suna so su shiga wata ƙasa ta daban, wannan abu ne da ya shafe su, amma dole ku kawar da su daga dazukanmu yadda ba za mu sake samu wasu ‘yan Boko Baram da za su addabe mu ba,” in ji Laftanar Janar Luyede.

Rahotanni sun nuna cewa ‘yan ƙungiyar Mahmuda sun samu mafaka ne a Gandun Dajin Kainji Lake National Park, inda daga can ne suke kai hare-hare a garuruwan da ke maƙwabtaka da dajin har ma da wasu yankuna na Jihar Neja mai maƙwabtaka.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#