Sport
Dollar
38,4292
0.2 %Euro
43,8350
-0.02 %Gram Gold
4.095,0600
-0.84 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Ma'aikatan NiMet suna yajin aiki ne saboda rashin aiwatar da sabon albashi mafi ƙanƙanta a ma'aikatarsu.
Jigilar matafiya a filayen jiragen saman Legas da Abuja da Kano ta fuskanci tsaiko a ranar Laraba yayin da ma’aikatan hukumar hasashen yanayi ta Nijeriya (NiMET) suka gudanar da zanga-zanga a filayen jiragen saman.
A filin jiragen saman Legas, rahotanni sun ce ma’aikatan jiragen XEJET da Aero Contractors sun yi aiki yadda aka tsara, yayin da Air Peace bai yi aiki yadda aka tsara ba.
A wata sanarwar da ya wallafa a shafinsa na X, kamfanin Air Peace ya bayyana cewa ya zama dole ya dakatar da jigilar matafiya domin yajin aikin da ma’aikatan NiMet suka fara.
Sanarwar wadda, mai magana da yawun kamfanin, Ejike Ndiulo, ya sanya wa hannu ta ce, “Saboda yajin aikin ma’aikatan NiMet da ake yi da kuma rashin samun rahoto kan yanayi da zai sa jirgi ya sauka lafiya, Air Peace ya dakatar da dukkan jigilar matafiya a faɗin ƙasar har zuwa ƙarshensa [yajin aikin].
“Amincinku shi ne abin da muka fi bai wa fifiko. Mun gode da fahimtarku, kuma za mu ci gaba ba da ƙarin bayani game da yadda abubuwa ke wakana.”
Domin magance matsalar, ministan sufurin jiragen sama da kula da sararin samaniya, Festus Keyamo, ya kira wata ganawa da ‘yan ƙungiyar ƙwadagon ma’aikatan NiMet da ke zanga-zanga. Za a yi zaman yau Alhamis.
A filin jiragen saman Nnamdi Azikiwe International Airport na Abuja, an fara yajin aikin ne da misalin ƙarfe 7:00 na safiya ranar Laraba, inda ma’aikatan NiMet da ‘yan ƙungiyar suka yi ta kai komo a cikin filin jiragen saman.
Rahotanni sun ce ma’aikata sun kwana a cikin ofishin hukumar ne domin tabbatar da cewa sun hana aiki gaba ɗaya.
A filin jiragen saman Mallam Aminu Kano da ke Kano, kuma fasinjoji da yawa ne suka kasa tafiya saboda zanga-zangar ma’aikatan NiMet da suke yi saboda rashin ƙaddamar da sabon albashi mafi ƙaranci a tsarin biyan albashinsu.
Zangar-zangar ta jinkirta tafiye-tafiye da yawa a filin jiragen saman, lamarin da ya sa mahukunta filin jiragen saman suka jikirta ko kuma soke tashin wasu jirage a filin jiragen.
Comments
No comments Yet
Comment