Dollar

38,4244

0.22 %

Euro

43,7464

-0.06 %

Gram Gold

4.059,2900

-1.7 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Yajin aikin ma’aikatan hukumar NiMET ya kawo tsaikon kwana biyu na sufurin jiragen sama a Nijeriya.

Ma’aikatan hukumar NiMet sun janye yajin aiki a Nijeriya

Ma’aikatan hukumar hasashen yanayi ta Nijeriya (NiMET) sun janye yajin aikin da suka shiga ranar Laraba wanda ya haddasa tsaiko a sufurin jiragen sama a faɗin ƙasar.

Ma’aikatan sun yi zanga-zanga ne game da yanayin aiki mai tattare da matsaloli, lamarin da ya sa suka hana tashin jirage.

Amma bayan sun gana da Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo a Abuja, sun janye yajin aikin.

Ma’aikatan sun nuna damuwa game da rashin soma biyansu sabon tsarin albashi mafi ƙanƙanta, kuma aka ƙi saka sunayen wasu ma’aikatan da aka tsallake wajen biyan alawus-alawus a baya tare da watsi da muhimman tsare-tsaren horaswa da sauransu.

  Zaman ya samu halartar babban daraktan hukumar hasashen yanayin Nijeriya NiMET da jami’an hukumar kula da sufurin saman Nijeriya (NCAA) da kuma ƙungiyar ƙwadagon sufurin Nijeriya da sauran masu ruwa da tsaki.

Kazalika a cikin mahalarta taron akwai haɗaɗɗiyar ƙungiyar ƙwadagon ma’aikatan kamfanonin gwamnati da ƙungiyar ƙwadagon ma’aikatan gwamnati da kuma ma’aikatan fasaha da ƙungiyar ƙwadagon ƙwararrun sufurin sama da kuma ƙungiyar ƙwadagon ma’aikatan sufurin sama.

Yajin aikin ma’aikatan hukumar NiMET ya kawo tsaiko a sufurin jiragen sama na ƙasar.

Yajin aikin da ya kai na kwanaki biyu ya sa matafiya da dama sun maƙale a filayen jiragen sama na ƙasa da ƙasa na Nnamdi Azikiwe da ke  Abuja da na Murtala Muhammed  da ke Legas da sauransu.

‘Aminci dai’

Kamfanin jiragen sama na Air Peace ya sanar da fasinjojinsa cewa jiragensa ba za su tashi ba saboda yajin aikin.

A ranar Laraba, shugaban kamfanin Air Peace, Allen Onyema, ya ba da umarnin soke tashin dukkan jiragensa a faɗin ƙasar.

“Idan NiMET ba ta janye yajin aikin ba, ku soke duk wata tafiye-tafiyen jiragen Air Peace a yanzu nan take. Rayukan mutane da amincin kayyayakinmu da kuma ma’aikatanmu su ne kan gaba,” in ji shi.

“Ban damu ba idan sauran kamfanonin jiragen sama na jigila. Ku katse duk tafiyar jiragen Air Peace a fadin ƙasar. Dubi yadda ake tsawa a ko ina. Dubi irin yanayin da muke shiga cikinsa kuma hukumar NiMET, wadda ya kamata ta ba da waɗannan [bayanan yanayi] tana yajin aiki, kuma jirage na tashi,” in ji shi.

“Ku katse dukkan tafiyar jirage nan take, har zuwa lokacin za a sake ba da ƙarin bayani, har zuwa lokacin da yajin aikin zai ƙare. Aminci ne a kan gaba.”

Ana ganin jiragen za su soma aiki yanzu da ma’aikatan hukumar sun janye yajin aikinsu.

 

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#