Dollar

38,4292

0.2 %

Euro

43,8350

-0.02 %

Gram Gold

4.095,0600

-0.84 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Mataimakin shugaban ƙasar Nijeriya ya ce sa bakinsa ne ya sa aka soke shirin bai wa mahajjata kuɗaɗen guzurinsu ta katin ATM.

Za a bai wa mahajjatan Nijeriya kuɗaɗen guzurinsu a hannu ne, maimakon a ATM —Shettima

Matakaimakin Shugaban Nijeriya, Kashim Shettima, ya ce a yanzu za a bai wa mahajjata kuɗaɗen guzurinsu a hannu ne, maimakon yadda tun da farko ake so a ba su ta katin ATM.

 A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Shettima ya ce an cim ma wannan matsayar ne a lokacin da ya gana da jami’an hukumar jin ɗaɗin alhazai ta ƙasa da jami’an babban bankin Nijeriya (CBN) ranar Laraba.

“Bayan zaman ne CBN ya amince da buƙatar bai wa maniyyata damar riƙe takardun kuɗi wajen sauke farali a Makkah,” in ji Shettima.

“Damuwa ta bazu cikin jama’a sosai cewa shawarar wajabta amfani da katin cire kuɗi da CBN ya yi wa mahajjata za ta iya kawo tangarɗa kan shiryawa da kuma aiwatar da aikin Hajjin shekarar 2025,” in ji sanarwar tasa.

Ya bayyana cewa da farkon wannan shekarar ne CBN ya gyara hanyar ba da kuɗin guzuri (BTA) ga ‘yan Nijeriya da za su yi Hajjin shekarar 2025.

A ƙarƙashin sabon shirin CBN zai bai wa ko wane maniyyaci katin ATM domin cire kuɗi da kuma sayayya a lokacin da suke Saudiyya, in ji Shettima.

Wannan shirin kuma zai tilasta wa dukkan maniyyaci ya buɗe asusun ajiya da ke haɗe da kuɗin guzuri (BTA).

Sai dai kuma sa bakin mataimakin shugaban ƙasa ya sa an sauya wannan shirin kuma maniyyatan za su tafi da takardun kuɗaɗensu ne a hannu.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#