Sport
Dollar
38,4292
0.2 %Euro
43,8350
-0.02 %Gram Gold
4.095,0600
-0.84 %Quarter Gold
0,0000
%Silver
0,0000
%Shugaban Turkiyya ya yi kira ga matasa su mutunta sadaukarwar da magabata suka yi, da jajircewa da haɗin kai — yana mai haɗa jiya da fatan Turkiyya na gobe.
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi bikin tunawa da cika shekaru 110 da yaƙin Canakkale ko Gelibolu, yana mai haskaka muhimmancin abinda ya kira “Jarumtar Canakkale”
A ranar Juma’a, ya ce ƙarfin gwiwa da haɗin kai da jajircewar da Turkiyya ta nuna a lokacin yakin Gelibolu, na ci gaba da zama jagora ga ƙasar a yau.
Erdogan ya jaddada cewa a yanzu alhakin na kan matasa da su yi aiki da saƙon ‘yancin kai da juriyar da ke cikin tarihin ƙasar.
Ya ƙara da cewa ya zama dole a dinga tunawa da sadaukarwar da aka yi a Gelibolu tare da girmama ta ta hanyar tabbatar da an kare waɗannan darajoji tare da kai su ga zamaninnika masu zuwa a nan gaba.
Shekaru 100 na Turkiyya
Da yake danganta jajircewar ƙasar a tarihance da inda ƙasar ta sa gaba a yanzu, Erdogan ya yi nuni ga fatan “Turkiyya nan da Shekaru 100” masu zuwa, a matsayin wani ruhi na zamani da ke haska irin nasarar da aka samu a Canakkale
Ya ce manufar ita ce a kalli daraja da girman magabata da suka tunkari duk wani ƙalubale tare da sauya tarihi ta hanyar cin nasarar yaki kan sojojin manyan ƙasashen duniya a wancan lokacin.
Duk da ƙalubalen da ake ci gaba da samu a duniya a yau, Erdogan ya sake jaddada ƙudirin Turkiyya na maye gurbin yaki, da ta’addanci da rikici zuwa zaman lafiya da walwala da girmama ɗan’adam. Ya bayyana haka a matsayin gwagwarmayar da ƙasarsa ke ci gaba da yi don tabbatar da adalci da kare ɗan’adam.
Girmama waɗanda suka kafa ƙasa
Shugaban Kasar ya ƙarƙare jawabin nasa da yaba wa jaruman yakin Gelibolu musamman Gazi Mustafa Kemal Ataturk.
Ya mika saƙon gaisuwa ga dukka ‘yan ƙasar Turkiyya, inda ya yi kira da a yi aiki da ɗabi’un da aka ɗabbaka a ɗaya daga zamuna mai muhimmanci ga ƙasar.
Comments
No comments Yet
Comment