Sport
Dollar
38,0146
0.27 %Euro
42,0297
-0.03 %Gram Gold
3.781,4500
-0.4 %Quarter Gold
6.314,4100
0.15 %Silver
37,8100
-2.69 %Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya jaddada buƙatar gagarumin haɗin kai da ƙasashen da ba na EU ba a harkar tsaron Turai.
Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya gana da takwaransa na Faransa Jean-Noel Barrot a birnin Faris, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi ƙasashen biyu da kuma yankin.
A cewar majiyoyin Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya, a ranar Larabar, ƙasashen biyu sun tattauna batutuwa daban-daban yayin ganawar tasu.
An ce Fidan ta bayyana mahimmancin haɓaka haɗin kai tare da ƙasashen da ba na EU ba wajen tsara sababbin tsare-tsare na tsaron Turai.
Har ila yau, ya bayyana fatan Turkiyya na cewa Faransa za ta goyi bayan kawar da shingen wucin-gadi da ke kawo cikas ga dangantakar Turkiyya da EU, kuma EU za ta ɗauki ƙwararan matakai kan wannan al'amari. An kuma tattauna batun sabunta haɗakar fiton kaya ta Turkiyya da EU ta shekarar 1995.
Kokarin kawo ƙarshen rikice-rikice
Fidan ya jaddada goyon bayan Turkiyya ga ƙoƙarin diflomasiyya a kawo ƙarshen yaƙin Rasha da Ukraine tare da jaddada muhimmancin haɗin gwiwa a tsakanin dukkanin ƙawancen NATO a cikin wannan tsari.
Ya kuma jaddada cewa, duk wata hanyar da za a iya kawo masalaha, dole ne ta sami amincewar ɓangarorin biyu don samun ɗorewa.
Dangane da ƙasar Siriya, Fidan ya bayyana buƙatar ƙara cuɗanya da sabuwar gwamnatin ƙasar, tare da yin kira da a ɗage takunkuman da aka sanya mata gaba ɗaya, domin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Ya bayyana fatan Turkiyya game da haɗin gwiwar masana'antar tsaro tare da jaddada muhimmancin yaƙar kungiyar ta'addanci ta PKK/YPG.
Fidan ya kuma ce, ya kamata a mayar da 'yan ta'addar Daesh 'yan ƙasashen waje da ke tsare a gidajen yari da sansanonin da ke arewacin Siriya ƙasashensu na asali.
Rikicin Isra'ila a Gaza
Dangane da barazanar tsaron yakin ta hare-haren da Isra'ila ke ci gaba da kai wa Gaza, Fidan ya yi gargaɗin cewa za su iya haifar da rashin zaman lafiya a yankin, tare da jaddada adawar Turkiyya ga duk wani yunƙurin tilastawa Falasɗinawa gudun hijira daga mahaifarsu.
Ya sake jaddada goyon bayan Turkiyya ga shirin Gaza da Ƙungiyar Haɗin Kan Larabawa ta amince da shi, inda ya ƙara da cewa, hana kai agajin jin kai da Isra'ila ke yi a Gaza yana ƙara ta'azzara matsalar jin ƙai.
Ya jaddada muhimmancin tabbatar da kai kayan agaji ba tare da katsewa ba zuwa Gaza.
Fidan da Barrot sun kuma tattauna kan ƙoƙarin samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Caucasus.
Ɓangarorin biyu sun yi nazari kan matakan ƙarfafa dangantakar tattalin arziki da kuma duba damar yin haɗin gwiwa a fannin makamashi.
Dangane da abubuwan da suke faruwa a baya bayan nan a Turkiyya, Fidan ya soki yadda ake amfani da wasu matakai daban kan Turkiyya tare da jaddada cewa ya kamata a ƙyale ɓangaren shari'a su gudanar da ayyukansu, kamar yadda aka gani kwanan nan a Faransa da Romania.
Fidan ya kuma ce, Turkiyya na sa ido sosai kan abubuwan da ke faruwa a Faransa.
Comments
No comments Yet
Comment