Sport
Dollar
38,1588
0.3 %Euro
43,6101
1.61 %Gram Gold
3.958,7400
2.25 %Quarter Gold
6.529,2600
2.67 %Silver
39,4700
3.6 %A makon da ya gabata ne aka kama babban kwamandan 'yan a-waren arewacin Mali a Nijar, kamar yadda jami'an tsaron yankin suka sanar da AFP.
Wata majiyar tsaro ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa jami’an tsaron Nijar sun kama Inkinane Ag Attaher wanda Ƙngiyar ‘Yantar da Abzinawa (FLA) ta bayyana a matsayin ‘kwamanda’, wanda ke da alhakin kula da horar da mayaƙa.
“An yi kamen na Nijar a tsakanin yankin Dosso da birnin Konni, a kudancin Nijar da ke iyaka da Nijeriya,” in ji wata majiyar abzinawa, kamar yadda ta shaida wa AFP.
Nan da wani dan lokaci Bamako za ta nemi a mayar mata da shi zuwa Mali, in ji wata majiyar a ƙasar Mali.
A ƙarshen shekarar da ta gabata ne aka ƙirƙiri Ƙungiyar ‘Yantar da Abzinawa inda aka haɗe ƙungiyoyin Abzinawa da ke kokarin ƙwace wasu yankunan arewacin Mali.
Nijar da Burkina Faso da Mali sun kafa Ƙawancen Ƙasashen Sahel (AES), kuma sun fara da ƙulla yarjejeniyar tsaro a 2023.
“A wajenmu, dan ta’adda ne,” in ji majiyar ta Njar, tana mai ƙara wa da cewa wanda ake zargin yana da fasfo na kasashe biyu a lokacin da aka kama shi - ɗaya na Nijar ɗaya na Mali.
Attaher ya bar rundunar sojin Mali, inda a 2012, ya shiga Kawancen ‘Yantar da Abzinawa (MNLA), wani ɓangare da ya ɓalle daga ‘yan aware da ya kori sojoji daga yankunan arewacin Mali da dama.
Tun bayan hawa mulki, gwamnatin Mali ta kawo karshen ƙawacen ƙasar da tsohuwar ‘yar mulkin mallakarta Farasa da kawayenta na Turai.
‘Yan awaren sun ci gaba da kai wa sojoji da gwamnati hare-hare a a daidai lokacin da gwamnatin Mali ta kori shirin ajalisar Ɗinkin Duniya na daidaita al’amura.
Tun daga nan, ‘yan a-waren masu ɗauke da makamai suka rasa iko da garuruwa da dama a arewaci, bayan hare-hare da sojojin Mali suka ringa kai musu, wanda har ya kai ga ƙwace birnin Kidal, wajen da ya zama alamar ‘yanci kuma ya zama wani babban waje na nuna cin gashin kan gwamnatin ƙasar.
Comments
No comments Yet
Comment