Sport
Dollar
38,1245
0.1 %Euro
43,3070
0.61 %Gram Gold
3.973,2800
0.46 %Quarter Gold
6.511,6500
0 %Silver
39,6100
0.03 %Atisayen wanda za a shafe kwanaki shida ana gudanar da shi mai suna AIKEYME, an ƙaddamar da shi ne a ranar Lahadi kuma rundunar sojin India da kuma rundunar tsaron Tanzania ta TPDF.
Indiya da ƙasashen Afirka da dama sun ƙaddamar da wani atisaye na musamman a birnin Dar es Salaam da ke Tanzania, wanda hakan ke alamta wani babban ci gaba ga ɓangaren alaƙa ta ɓangaren tsaro tsakanin Indiya da Afirka.
Atisayen wanda za a shafe kwanaki shida ana gudanar da shi mai suna AIKEYME, an ƙaddamar da shi ne a ranar Lahadi kuma rundunar sojin India da kuma rundunar tsaron Tanzania ta TPDF.
Sojoji daga ƙasashen Comoros, Djibouti, Kenya, Madagascar, Mauritius, Mozambique, Seychelles, Afirka ta Kudu, Indiya da kuma mai masauƙin baƙi wato Tanzania.
“Wannan atisayen na nuni da jajircewarmu wurin tabbatar da zaman lafiya da tsaro a yankin Tekun India,” in ji sanarwar da rundunar sojin ruwa ta Indiya ta fitar.
“Yana ƙarfafa damar da ake da ita ta haɗin gwiwa domin daƙile barazana a cikin teku da kuma ƙarfafa dangantakar yanki.”
‘Sabon babi’
Jiragen ruwa na yaƙi na INS Chennai na Indiya mai kakkaɓo makami mai linzami da INS Kesari wanda ke dakon tankar yaƙi na daga cikin manyan mahalarta atisayen, wanda ke daya daga cikin manufofin tsaro da ci gaba na Indiya.
Ministan tsaron Tanzaniya Stergomena Lawrence Tax, wanda ƙasarsa ta ɗauki nauyin taron, ya yi jawabi a cikin jirgin INS Chennai inda ya yi jinjina ga “sabon babi” a haɗin kai ta ɓangaren tsaro tsakanin Indiya da Afirka.
"A cikin waɗannan lokutan da ba a tabbatar da su ba, haɗin gwiwar yanki ba na zaɓi ba ne - wajibi ne," in ji Tax ga manema labarai.
"Wannan atisayen yana ba mu damar horarwa tare, shirya tare da aiki tare lokacin da bukatar hakan ta taso. Muna alfahari da kasancewa cikin wannan lokacin tarihi."
“A cikin irin wannan lokaci na rashin tabbas, haɗin kan yanki a halin yanzu ba zaɓi bane – dole ne,” kamar yadda Tax ya shaida wa manema labarai.
“Wannan zai ba mu damar yin atisaye a tare, shiri tare da kuma aiki tare idan buƙatar hakan ta taso. Muna alfahari da kafa wannan tarihi.”
Comments
No comments Yet
Comment