Dollar

38,4292

0.2 %

Euro

43,8350

-0.02 %

Gram Gold

4.095,0600

-0.84 %

Quarter Gold

0,0000

%

Silver

0,0000

%

Sanarwar ta ce kamfanin Meta mamallakin Facebook da WhatsApp ya kai ƙara kotun ne bayan hukumomin ƙasar sun ci shi tarar dala miliyan 220 bisa ƙeta dokokin Nijeriya.

Kotu ta amince da tarar dala miliyan 220 da Nijeriya ta ci Facebook da WhatsApp

Wata kotu ta musamman kan gasa da kare masu sayayya ta amince da tarar dala miliyan 220 da Hukumar Gasa da Kare Haƙƙin masu sayayya Nijeriya (FCCPC) ta ci shafukan sada zumunta na Facebook da WhatsApp.

Wata sanarwa da daraktan watsa labaran hukumar ta FCCPC, Ondaje Ijagwu, ya fitar wadda mataimaki na musamman ga Shugaba Tinubu kan dabaru da watsa labarai, Bayo Onanuga ya wallafa a shafinsa na X, ce ta tabbatar da lamarin.

Sanarwar ta ce kamfanin Meta mamallakin Facebook da WhatsApp ya kai ƙara kotun ne bayan hukumar ta ci shi tarar dala miliyan 220, bisa ƙeta dokokin Nijeriya.

Kotun “ta yanke hukuncin cewa WhatsApp da Meta sun ƙeta dokokin Nijeriya” kamar yadda hukumar FCCPC ta bayyana, kuma hukumar ba ta yi laifi ba, in ji sanarwar.

Alƙalai uku ne suka jagoranci kotun ƙarƙashin jagorancin Thomas Okosun. Yayin da farfesa Gbolahan Elias ya jagoranci lauyoyin WhatsApp da Meta, Babatunde Irukera ne ya jagoranci lauyoyin hukumar FCCPC.

A ranar 19 ga watan Yulin shekarar 2024 ne dai hukumar FCCPC ta ba da umarni na ƙarshe ga Meta kan ya biya tarar dala miliyan 220 ɗin, bayan ta tabbatar da cewa kamfanin yana aikata laifukan wariya da ci-da-gumin ‘yan Nijeriya masu hulɗa da shi.

Tun a shekarar 2020 hukumar tare da haɗin gwiwar Hukumar Kare Bayanai ta Nijeriya suka fara bincike kan zargin yadda kamfanin na Meta yake mu’amala da bayanan masu hulɗa da shi da ma tsare-tsarensa kan bayanan abokan hulɗa.

A bara ne kuma kamfanin na Meta ya nuna rashin amincewa da matakin sanya masa tara, inda ya garzaya kotun ta musamman yana ƙalubalantar sanya masa tara a shari’ance, da kuma sakamakon binciken da hukumomin suk ayi.

Sai dai yayin da take yanke hukunci kan ƙarar, kotun ta tabbatar da hanyoyin da hukumar ta FCCPC ta bi wajen binciken.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#