Sport
Dollar
38,1250
0.08 %Euro
43,5070
1.04 %Gram Gold
4.009,0200
1.36 %Quarter Gold
6.511,6500
0 %Silver
39,7400
0.36 %An haramta wa wani masoyin Manchester United da ya mari Jack Grealish, ɗan wasan Manchester City shiga filin wasa na Old Trafford, bayan an kama shi da laifin cin mutunci.
Manchester United ta haramta wa wani magoyin bayanta shiga filin wasanta na Old Trafford, saboda zarginsa da marin ɗan wasan Manchester City, Jack Grealish bayan wasan da ƙungiyoyin biyu suka buga ranar 6 ga Afrilu.
Lamarin ya faru ne bayan an busa usur ɗin ƙare wasan na Gasar Firimiya, wanda aka tashi canjaras babu ci 0-0.
Ɗan wasan gaba na Man City Jack Grealish ya kama hanyar fita daga filin don shiga masaukin ‘yan wasa, sai wani matashi mai suna Alfie Holt, mai shekaru 20 ya nemi ɗan wasan ya matso kusa inda ya gaura masa mari.
Bayan faruwar lamarin, ‘yan sanda sun shiga bincike inda ita kuwa United ba ta ɓata lokaci ba wajen haramta wa matashin halartar wasannin ƙungiyar nan gaba a filin wasanta na Old Trafford.
Haramcin yana da nufin nuna rashin sassauci kan ɗabi’ar rashin kyautawa daga magoya baya da masu zuwa kallon wasan ƙwallo.
Jawabin ‘yan sanda
Wani jami’in ‘yan sanda na Greater Manchester ya fitar da sanarwa kan lamarin mai cewa, "An tuhumi Alfie Holt, mai shekara 20, daga Droylsden kan zargin laifin kai farmaki.
“Zai bayyana gaban kotun majistire ta Manchester a watan Yuli. Tuhumar tana da alaƙa da abin da ya faru a Old Trafford.”
Wasu da suka san Holt sun nuna al’ajabi da jin labarin, inda suka bayyana matashin da kyawawan ɗabi’u.
Bayan faruwan lamarin, babu rahoton cewa Grealish ya samu rauni. Amma ban da shi akwai wani ɗan wasan Man City, Phil Foden wanda ya sha zagi daga rumfar magoya bayan Man United yayin wasan.
Comments
No comments Yet
Comment