Sport
Dollar
38,1283
0.1 %Euro
43,4090
0.64 %Gram Gold
3.973,1800
0.45 %Quarter Gold
6.511,6500
0 %Silver
39,6200
0.07 %Yayin da rahotannin ke cewa Manchester United ta fasa yin gwanjon mai tsaron gidanta Andre Onana, a yanzu ta rage wa 'yan wasanta albashi da kashi 25 cikin 100.
Rahotanni daga Manchester United na cewa babban mai tsaron gidan ƙungiyar, Andre Onana ya ji mamaki kan matakin da aka ɗauka na rage masa albashi da kasi 25 cikin 100.
Hakan na zuwa ne bayan ta tabbata cewa United ba za ta buga gasa a Turai ba a kaka mai zuwa, saboda gazawarsu na zama cikin ƙungiyoyi biyar na saman teburin gasar Firimiya a bana.
Bayanai sun ƙara da cewa Onana ya nemi yin tattaunawa da daraktan wasanni na ƙungiyar, Dan Ashworth, kan batun kwantiraginsa.
Yayin da ya rage wasanni shida a kammala gasar ta ba Firimiya, United wadda ke da maki 38 daga wasanni 32, ba za ta samu gurbin buga kowace gasa a Turai ba a baɗi.
Ko a bara ma, United ta kammala gasar Firimiya a mataki na takwas ne, wanda ke nufin ba za ta iya buga gasannin Turai a bana ba, amma dai ta samu damar buga gasar Europa saboda lashe kofin FA na Ingila.
Zaftare albashi
Kwantiragin ‘yan wasan Manchester United ya tanadi zaftare albashin ‘yan wasa da kashi 25% a wannan shekarar. Kuma ba Onana kawai abin ya shafa ba.
A bazarar bara, an ruwaito Onana wanda ya yi wasa a Ajax da Inter, yana sha’awar komawa Saudiyya da taka leda. Amma sai aka ga ya sayi gida a garin Manchester, wanda ya nuna ƙudurinsa na zama a United.
Onana dai yana shan suka saboda kurakuran da yakan tafka a ayyukansa na tsaron gidan United. Ya yi ƙaurin suna saboda yawan shirme, tun zuwansa United a 2023 inda ya maye gurbin David de Gea.
Mai shekaru 29, Onana ya tafka kurakurai a wasan Man U da Lyon, wanda ya janyo koci Ruben Amorim ya cire shi daga tawagarsa a wasan da Newcastle ta doke su da ci 4-1.
Bayan nan an ruwaito cewa United ta fitar da rai daga Onana, kuma tana duba yiwuwar sayar da shi a bazara mai zuwa.
A yanzu dai ana sa ran Onana zai iya samun damar komawa tawagar a wasan zagaye na biyu da za su buga da Lyon a gasar Europa matakin kwata-fainal.
Comments
No comments Yet
Comment