Dollar

38,1208

0.08 %

Euro

43,4932

0.95 %

Gram Gold

4.020,0400

1.64 %

Quarter Gold

6.511,6500

0 %

Silver

39,7900

0.49 %

Tauraron Liverpool, Mohamed Salah ya tsawaita zamansa a Liverpool, ya sanya hannu kan sabuwar kwantiragi.

Mohamed Salah ya karɓi sabuwar kwantiragi a Liverpool

Dan wasan gaba na Liverpool ɗan asalin Masar, Mohamed Salah, ya sanya hannu kan sabuwar kwantiragi wadda za ta tsawaita zamansa a Liverpool, inda ya yi shekaru takwas zuwa yanzu.

Salah ya faɗa a wata sanarwa cewa, “Tabbas ina matukar farin ciki. Muna da gagarumar tawaga yanzu.

A baya ma muna da ƙungiya mai kyau. Amma na sanya hannu ne saboda na yi imani cewa muna da damar lashe ƙarin kofuna kuma in ji daɗin ƙwallona”.

“Abun ƙayatarwa ne; na samu mafi kyawun shekaruna a nan. Na buga wasa shekaru takwas. Ina fatan zai kai shekaru 10.

“Ina jin daɗin rayuwata a nan, ina jin daɗin ƙwallon ƙafa ta. Na samu mafi kyawun shekarun aikina a nan”.

Masana suna kallon wannan a matsayin babban cigaba ga Liverpool, musamman ganin Salah yana kan ganiyar tagomashi a kakar bana, inda yake taimakawa ƙungiyarsa wajen jan ragamar teburin Firimiya da take damar lashe kofin Firimiya na 20.

Salah mai shekaru 27 ya ci ƙwallaye 27 da tallafin ƙwallo 17 a gasar Firimiya ta bana.

A zamansa a Liverpool, Mohamed Salah ya lashe Gasar Firimiya, da ta Zakarun Turai, da Kofin FA kuma Kofin Carabao. Sannan ya lashe Kofin UEFA Super Cup da FIFA Club World Cup.

Comments

Comment

Comment Your email address will not be published. Required fields are marked*

No comments Yet

#