Sport
Dollar
38,0243
0.1 %Euro
41,5020
0.03 %Gram Gold
3.647,5800
0.17 %Quarter Gold
6.187,2600
0 %Silver
36,8000
0.05 %Kocin Southampton, Ivan Juric ya raba gari da ƙungiyar bayan da ta zama ta farko da ta rikito daga matakin gasar Firimiya.
Southampton ta Ingila ta zama ƙungiyar farko da ta rikito daga gasar Firimiya ta Ingila, inda ta kafa tarihin wadda ta fi saurin faɗowa, kuma za ta koma matakin ƙaramar gasar Championship a baɗi.
Bayan rashin nasarar da Southampton ta samu da ci 3-1 ranar Lahadi a hannun Tottenham, ta tabbata cewa ƙungiyar ba za ta iya fita daga ƙungiyoyi uku na ƙasan teburin gasar Firimiya ba, wanda ke nufin za ta bar gasar a ƙarshen kakar bana.
A tarihin gasar Firimiya, Southampton ce wadda ta fi saurin fita daga gasar tun ana mako na 31, wanda ya zamo abin takaicin da ya tilasta aka sallamin kocin.
A Disamban 2024 ne Juric ya maye gurbin Russell Martin a ƙungiyar, inda ya zo da burin ceto ta daga ruwa. Mai shekaru 49, Juric ya ci wasa ɗaya ne kacal tun zuwansa.
Bayan tabbatar da makomar ƙungiyar, an ambato Juric yana cewa, "A wajena, wannan wani sabon abu ne da ban taɓa fuskantar irinsa ba. Na gaya wa ‘yan wasana dole su yi alfahari da irin masoyan da suke da su”.
Sanarwar ƙungiya
A safiyar Litinin Southampton ta fitar da sanarwar tafiyar Ivan Juric tana mai cewa, "Muna tabbatar da cewa mun cim ma matsaya da kocin babbar ƙungiyarmu ta maza, Ivan Juric don kawo ƙarshen aikinsa a ƙungiyarmu”.
"Ivan ya zo Southampton ne a wani matsanancin yanayi da aka ba shi aikin ƙoƙarin inganta ƙungiyarmu. Sai dai kash, ba mu ga ci-gaba a ƙwazonmu ba kamar yadda muka yi fata, amma muna miƙa godiya ga Ivan da jami’ansa kan gaskiya da aiki tuƙuru wajen yaƙin ceto mu”.
"Yanzu mun fara neman sabon koci don jagorantar mu wajen gaggawar komawa gasar Firimiya, wanda daraktan wasanni Johannes Spors ke yi”.
Yayin da aka ayyana Simon Rusk a matsayin kocin riƙon-ƙwarya tare da Adam Lallana a matsayin mai taimaka masa, wasanni bakwai ne suka rage wa Southampton a kakar bana, inda take da maki 10 kacal.
Comments
No comments Yet
Comment