Sport
Dollar
38,0196
0.09 %Euro
41,7935
0.62 %Gram Gold
3.661,6900
0.56 %Quarter Gold
6.187,2600
0 %Silver
36,7700
-0.02 %Rahotanni sun bayyana cewa, ɗan wasan mai suna Gabriel Olanrewaju ya faɗi ne a yayin fafatawar wasan dambe na ƙasa da ƙasa da aka kara a ranar Asabar a Ghana.
Hukumar wasannin damɓen boksin ta Ghana (GBA) ta tabbatar da mutuwar ɗan wasan boksin na Nijeriya, Gabriel Oluwasegun Olanrewaju, wanda ya rasu a wata fafatawa a daren Asabar, 29 ga Maris, 2025.
Rahotanni sun bayyana cewa, ɗan wasan ya gamu da ajalinsa ne bayan ya faɗuwar da ya yi a yayin fafatawarsa da wasan ƙasar Ghana John Mbanugu a gidan damɓe na Bukom da ke birnin Accra.
Kazalika, a sanarwar da GBA ta fitar, ta ce dan wasan ya samu takardar shaidar koshin lafiya daga likita kafin soma wasan wanda ya ba shi damar karawa a wasan na ƙasa da ƙasa.
"Kafin fara wasan, hukumar damben boksin ta Nijeriya ta ayyana Oluwasegun a matsayin wanda ke da koshin lafiya tare da ba da shaida da ke nuna matsayinsa na kwararre a wasan damben boksin kafin hukumar ta GBA ta amince da gasar ta kasa da kasa," a cewar sanarwar.
Comments
No comments Yet
Comment