Sport
Dollar
38,0218
0.09 %Euro
41,8362
0.73 %Gram Gold
3.663,7400
0.62 %Quarter Gold
6.187,2600
0 %Silver
36,8100
0.09 %Wata doka ta Hukumar Ƙwallo ta Duniya, FIFA ta tanadi cewa Bayern Munich za ta iya neman a biya ta diyya kan raunin da ɗan wasanta Alphonso Davies ya samu a wasan da ya buga wa ƙasarsa Canada.
Ɗan wasan baya na Bayern Munich, Alphonso Davies ya samu rauni a wasan da ya buga wa tawagar ƙasarsa ta Canada.
Raunin da Davies ya samu ya sanya ƙungiyarsa ta Bayern za ta iya samun diyya daga FIFA, wadda za ta iya kai wa euro miliyan 7.5.
A watan jiya ne ɗan wasan ya sanya hannu kan sabuwar kwantiragi inda yake fatan taka leda son-ransa a kakar bana.
Davies wanda shi ne kyaftin ɗin tawagar Canada wadda ta doke tawagar Amurka da ci 2-1 ranar 23 ga Maris. Ya samu raunin da zai tilasta masa jinya har zuwa ƙarshen kakar bana.
Dokar diyya
A yanzu, shafin Goal ya ruwaito cewa Bayern Munich ta cancanci samun diyya daga FIFA, sakamakon cewa a wasannin ƙasa-da-ƙasa da FIFA ta shirya ne ya samu raunin.
Dokar FIFA ta Kare Muradun Ƙungiyoyi ta tanadi biyan diyya ga ƙungiyar da ta rasa ɗan wasa da ya je buga wa ƙasarsa a wasannin da FIFA take shiryawa.
Ana ƙirga diyyar ta FIFA bisa la’akari da albashin ɗan wasan. Mafi girman diyyar da FIFA za ta biya ƙungiya shi ne euro miliyan €7.5.
Comments
No comments Yet
Comment